<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya ƙanƙanuwar Baitalahmi, can ƙasar Yahuda,
 Ba auta ba ce ko kaɗan cikin Yahudiya,
 Gama daga cikinki, Mai Ceto zai fito.
 Tauraronsa a bisanki, shi kansa cikinki.

[V2]
 2) Hanyoyinki dā duhu ne, yanzu ga haskensu.
 Dā, mutane sun raina ki, yanzu ga daraja.
 Ji waƙoƙin mala'iku, yabo ga Allahnmu
 A cikin mafi ɗaukaka, a duniya salama.

[V3]
 3) Shehunan gabas fa sun zo, sun kawo dukiya.
 Gaisuwa, girma, daraja, ga yaron aka bayar.
 Ga Yesu Mai Cetonmu a cikin Baitalahmi,
 Ba waninsa a duniya, Maɗaukaki ne shi.</lyrics>
<title>Ya Ƙanƙanuwar Baitalahmi, Can Ƙasar Yahuda LW79</title>
<hymn_number>79</hymn_number>
<author>Brooks, Phillips (1835-1893), Redner, Lewis Henry (1830-1908)</author>
</song>